Wannan ya faru ne a bayan da suka doke 'yan wasan kasar Ethiopia a zagaye na biyu na karawar da kasashen biyu suka yi domin zaben dayarsu da zata shiga cikin wakilan Afirka a wannan gasa ta duniya.
A karawar farko da aka yi cikin watan da ya shige a Addis Ababa, babban birnin Ethiopia ma, 'yan wasan na Super Eagles ne suka samu nasara da ci 2-1. Wannan na nufin cewa Najeriya ta lashe wannan karawa tsakaninsu da ci 4-1.