Tunisia Ta Fice A Gasar Cin Kofin Duniya Duk Da Ta Doke Faransa

Magoya bayan Tunisia suna kuka a gasar cin duniya a Qatar

Ita dai Australia ta doke Denmark ita ma da ci 1-0 a rukunin na D, hakan ya ba ta damar karbe matsayi na biyu a teburin rukunin da yawan kwallaye.

Faransa da ke rike da kofin duniya ta sha kaye a hannun Tunisia da ci 1-0.

Sai dai duk da wannan nasara da ta samu, ba ta kai ga shiga zagayen ‘yan 16 ba.

Wahbi Khazri ne ya zurawa Tunisia kwanllonta a minti na 58.

Ita dai Australia ta doke Denmark ita ma da ci 1-0 a rukunin na D, hakan ya ba ta damar karbe matsayi na biyu a teburin rukunin da yawan kwallaye.

Shi dai Khazri, sai da ya yi wuce ‘yan wasan Faransa biyu kafin ya doka kwallon a gefen ragar Faransa.

Wannan ita ce nasara ta uku da Tunisia ta samu a tarihin gasar cin kofin duniya.

Da farko, kocin Faransa Didier Deschamp ya ajiye Griezman da Kylian Mbappe da sauran ‘yan wasan da ya kan fara wasa da su, saboda sun riga sun tsallaka zagaye na gaba.

Amma kwallon Khazri ta zaburar da shi ya sako Griezman da Mbappe.

Griezman ya ci wata kwallo gab da ana shirin kammala wasan, amma an soke ta saboda alkalin wasa ya ce ya yi satar gida.