ya ga James Ibori, Barista Bala James Ngillari yanzu shine gwamna na biyu da kotu ta daure bisa zargin cin hanci da rashawa ko keta ka’idar aiki tun bayan da Najeriya ta koma tafarkin dimokaradiyya a 1999, batun da masu sharhi akan al’amurra ke ganin wannan hukuncin yana da muhimmanci da hakan ka iya zama darasi nan gaba.
Yanzu haka dai wannan batu dai shine ya dauke hankulan mutane a ciki da wajen Yola fadar jihar Adamawa, kasancewar yanzu haka akwai sauran tsofaffin gwamnonin jihar biyu dake gaban kuliya game da zargin laifuffukan da suka shafi cin hanci da rashawa.
Mallam Umar Dankano dake zama mataimakin shugaban kungiyar yan jarida ta jihar Adamawa na ganin akwai abin dubawa.
Shima wani mai sharhi da fashin baki kuma malami a kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Mallam Lawan Danladi, yace kukan kurciya aka yi.
Kotun dai ta yanke wa tsohon gwamnan jihar ne Bala James Ngillari, hukuncin daurin shekaru biyar a gidan Yari, saboda sabawa ka’idojin bayar da kwangila batun da masanin shari’a Barista Sunday Joshua Wigra ke ganin akwai abin dubawa.
Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.
Your browser doesn’t support HTML5