Wadanda suka jagoranci addu'ar ma shugaban Najeriya da zaman lafiyar kasar gaba daya sun bayyana dalilin da ya sa suka shiryata a daidai wannan lokacin da 'yan Najeriya ke cigaba da gudanar da addu'o'i a sassan kasar daban daban domin samun lafiyar shugaban kasar.
Alhaji Mustapha daya daga cikin jagororin da suka shirya addu'ar yace kowace yare na tare dasu suna addu'a. Su musulmi kansu na hade bisa ga yiwa kasa da shugaban kasa addu'a da yaransu da ma sauran addinai Allah ya sa su zauna lafiya da juna.
Alhaji Ahmadu Musa yace abun da ya kawosu wurin addu'ar shi ne yadda Najeriya da Nijar suke, wato tamkar Hassan ne da Hussaini. Duk abun da ya shafi Najeriya ya shafi Nijar. Inji Alhaji Musa dalili ke nan da duk shugabannin 'yan Nijar suka kasance a wurin addu'ar da fatan Allah ya ba Shugaba Buhari lafiya.
Duk wadanda suka yi magana fatansu guda ne, wato Allah ya tabbatarwa Shugaba Buhari lafiya ya kuma koma kasar Najeriya lafiya ya cigaba da ayyukansa.
Baicin yiwa shugaban kasa addu'a sun kuma roki Allah ya kawar da cin hanci da rashawa da matsalar sace mutane ana garkuwa dasu da fashi da makami da duk wani mugun hali da muggan mutane suke haddasawa.
Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.
Facebook Forum