Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ranar Wannan Larabar Za'a Rufe Filin Jirgin Saman Abuja


Daga hagu zuwa dama:Sanata Hadi Sirika, Rotimi Amaeci, Lai Muhammad, Ibrahim Idris
Daga hagu zuwa dama:Sanata Hadi Sirika, Rotimi Amaeci, Lai Muhammad, Ibrahim Idris

A wani mataki na bada tabbas rufewar filin jirgin saman Abuja ranar wannan Larabar takwas ga watan Maris na shekarar 2017ministan kula da harkokin sufurin jiragen sama Sanata Hadi Sirika yace titin sauka da tashin jirage yayi shekaru 30 ba'a taba yi masa kwaskwarima ba kuma ya soma zazzagewa.

Sanata Hadi Sirika yace suna da hujja babba na sake gina filin dake zama na kan gaba a harkar tsahi da saukan jirage na kasa da na kasashen waje.

Yace tsawon kilomita ukku ne da digo shida za'a gyara cikin makwanni shida kafin a sake bude filin. Gyaran zai ci kudi fiye da Nera biliyan biyar.

Dangane da jiragen kasashen waje ya musanta zargin cewa ma'aikatarsa basu yi taro da su ba. Hadi Sirika yace sun yi taro dasu ba iyaka. Sun ziyarci ofisoshin jakadancin da lamarin ya shafa inda suka yi cikakken bayani.

Yace akwai kasashen da suka ce zasu dinga zuwa suna sauka a Kaduna kamar yadda aka tanada. Jirgin kasar Turkiya da na Jamus da dai sauransu sun yi alkawarin sauka a Kaduna.

Gwamnatin Najeriya tace ta kammala shirin tsaro a sabon filin jirgin sama na Kaduna wanda aka yi masa gyara domin maye gurbin na Abuja cikin makwanni shidan da za'a yi ana gyara, inji babban sifeton 'yansandan Najeriya Ibrahim Idris.

A cewarsa yace sun baza 'yansanda da dama akan hanyar Kaduna zuwa Abuja tare da yin anfani da jirgi mai saukar angulu.

Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00

Facebook Forum

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG