Dalili ke nan da Majalisar Dinkin Duniya ko MDD take son matsalolin kasashen tafkin Chadin su fito fili domin a fahimcesu duniya da ma gwamnonin yankin su tashi a dauki matakan da suka dace kafin a makara.
Jagoran rangadin Matthew Rycroft shi yayi magana a taron manema labarai bayan dawowar tawagar daga Maiduguri wacce tun farko ta ziyarci Kamaru da Chadi da Nijar.
Matthew Rycroft shi ne jakadan Birtaniya a Majalisar Dinkin Duniya ko MDD yace cikin matsalolin akwai ta'adancin Boko Haram da MDD zata cigaba da dafawa yankin wajen kawo karshen matsalar gaba daya. Yace yana da kyau cikin kawar da ta'adancin a kuma shafe mummunar akidar Boko Haram tare da dawowa al'ummar yankin kyakyawar fata..
Hakan nan Rycroft yace baya ga wannan kalubale akwai damuwar 'yan gudun hijira inda mata da dama ke fama da kulawa da yara bayan an kashe mazajensu. Yace saboda haka MDD zata cigaba da samarwa yaran ilimi da abinci da kuma sake tsugunar dasu a garuruwansu na asali.
Shi ma jakadan Senegal a MDD yace duk yadda kasashen tafkin Chadin zasu so taimako sai sun fara tallafawa kansu da kansu. Ita wakiliyar Amurka a MDD din Michelle Simon tace a matsayin Amurka na kasancewa 'yar kwamitin sulhu zata cigaba da tallafawa yankin tafkin Chadi da kuma musamman rayuwar mata da yara.
Tace Amurka na yabawa kasashen ta fuskar shawo kan matsalolin saboda haka ma zata yi anfani da kungiyoyi masu zaman kansu wajen mika kayan agaji baya ga aiki da gwamnatocin yankin. Zuwa yanzu Amurka ta bada tallafin da ya kai dalar Amurka miliyan dari ukku da daya daga bara zuwa bana ga yankin.
Tawagar ta gana da majalisun tarayyar Najeriya sannan zata gana da Mukaddashin Shugaban Najeriya Farfasa Yemi Osinbajo kafin ta koma New York gobe domin kai rahoto wa babban sakataren majalisar Antonio Guterres.
Ga rahoton Nasiru Adamu Ek-Hikaya da karin bayani.
Facebook Forum