Tsohon Shugaban Nijar Na Fuskantar Barazanar Gurfana Gaban Hukumar Yaki Da Cin Hanci

Issouhou Mahamadou

A jamhuriyar Nijar gamayyar kungiyoyin fafutuka ta M-62 ta shigar da bukata a hukumar yaki da cin hanci, ta gurfanar da tsohon shugaban kasar Mahamadou Issouhou a gabanta.

Hukumar ta yi hakan ne domin ta binciki Issouhou Mahamadou kan wani binciken jami’an Amurka da Faransa ya gano cewa ya karbi kudi dalar Amurka million 2.6 a matsayin kamashon Ton 2,500 na ma'adanin uranium da aka sayar ta bayan fage da aka kitsa tsakanin kamfanin ORANO da wasu kamfanonin kasa-da-kasa.

Sai dai mukarraban tsohon shugaban kasar na cewa suna da kwarin guiwar ba abinda zai biyo baya.

Muhimmancin wannan badakala da ake yi wa lakabi da Uraniumgate da yadda sunan tsohon shugaban kasar Nijer ya bayyana a jerin wadanda suka yi ruwa da tsaki a wannan haraka ta bayan fage, ya sa gamayyar kungiyoyin farar hula ta M 62 gabatar da takardar bukatar ganin hukumar yaki da cin hanci ta kasa wato HALCIA ta gudanar da bincike domin gano gaskiyar lamari game da abinda ake zargin an kitsa a tsakanin shekarar 2012 da 2013 kamar yadda shugaban rikon kwaryar M-62 Sanoussi Mahaman ya bayyana.

Mukarraban tsohon shugaban kasar ta Nijar na ganin wannan yunkuri a matsayin maras tushe. Jigo a jam’iyar PNDS Tarayya Alhaji Assoumana Mahamadou wanda ke rike da mukamin mashawarci a fadar shugaban kasa a zamanin Issouhou Mahamadou ya kalubalanci wannan kungiya.

Tuni hukumar ta HALCIA ta karbi takardar ta M-62 saboda haka shugabanin kungiyar suka bukaci goyon bayan daukacin al’ummar Nijar su ba da kai don ganin an cimma nasarar wannan gwagwarmaya ta nema hasken abin da ke kunshe a badakalar, wacce ke daya daga cikin manyan badakalolin cin hancin da suka yi wa kasar tarnaki.

To sai dai magoya bayan jam’iyar mai mulki na alakanta yunkurin na ‘yan fafutika da wata boyeyiyar manufa, suna cewa ba su da fargaba game da abin da zai biyo bayan binciken da aka bukaci hukumar yaki da cin hanci ta aiwatar.

A karshen watan Afrilun 2023 ne jaridar Afrique Intelligence ta Faransa ta ruwaito labarin binciken da wasu jami’an Amurka da Faransa suka gudanar kan wata cinikyayyar bayan fagen da ta hada kamfanin ORANO da SOPAMINE da wasu kamfanonin kasashen Turai.

Million 101 na dolar Amurka ne aka karkasa bayan sayar da ton 2,500 na uranium.

Saurari rahoton a sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

SHIGAR DA KARAR ISSOUHOU MAHAMADOU GABAN HALCIA .mp3