Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Zargin Tsohon Shugaban Nijar Issouhou Mahmadou da Hannu A Badakalar Ureniungate


Shugaba Issouhou Mahamadou
Shugaba Issouhou Mahamadou

Wani binciken kasa da kasa ya bankado bayanan dake nuna alamun hannun tsohon shugaban kasa Issouhou Mahamadou a badakalar da karkashinta ake zargin mahukuntan Nijer sun hada kai da kamfanin Areva don sayar da tonne 2500 na karfen uranium ta bayan fage a shekarar 2011.

Binciken hadin guiwar da jami’an Amurka da na Faransa suka gudanar kan harkokin kamfanin OKI GENERL TRADING da ke da rajista a Dubai amma kuma ya ke da ofishi a jihar Virginia ta kasar Amurka , ya bada damar gano hannun wannan kamfanin a sahun wadanda suka karbi wani kaso daga kudaden cinikayyar tonne 2500 na karfen Uranium da kamfanin Areva ya sayar ta bayan fage da hadin kan kamfanin dillacin ma’adanai SOPAMINE na kasar Nijer, ta hanyar kamfanin Energy Stantard Trading FZE da nufin kauce wa hanyoyin biyan haraji a shekarar 2011.

Daga cikin million 101 na dalar Amurka na wannan hada hada, ana zargin tsohon Shugaban Nijer Issouhou Mahamdou da karbar million 2.6 na dalar a matsayin nasa kason, inda aka sakaya sunansa da wata lamba T3. Abinda kungiyar ROTAB mai fafutikar ganin an yi haske akan sha’anin ma’adanai ta ce, gaskiya ce ta yi halinta kamar yadda wani jigonta Boubacar Iliassou ya shaidawa Muryar Amurka a wata hira dangane da rahoton.

Wannan Badakala da aka yi wa lakanin “Uranium gate” ta haifar da dambarwa a shekarar 2012 inda wasu majiyoyi suka ce shugaban ma’aikata a fadar shugaba Issouhou na wancan lokaci, wato Hassoumi Massoudou ne ya wakilci Nijer a yayin zaman saka hannu kan wannan harka sai dai mahukunta suka musanta. Kasancewar batun ya sake farfadowa kungiyar ROTAB na ganin lokaci ya yi da za a bai wa kotu dama ta yi aikinta.

To amma wani mashawarcin shugaba Issouhou Mahamadou a zamanin da yake shugabancin kasa, Alhaji Assoumana Mahamadou na alakanta bayanan wannan bincike da abinda ya kira yunkurin shafa masa kashin kaji. A cewarsa masu tababa akan tsohon shugaban shugaban kasar ta Nijer su garzaya kotu.

Hukumar Sadarwa Ta Nijar Na Gudanar Da Zaman Taron Tattauna Muhimman Ayyukan Watsa Labarai
Hukumar Sadarwa Ta Nijar Na Gudanar Da Zaman Taron Tattauna Muhimman Ayyukan Watsa Labarai

Ainihi binciken neman haske kan kadarorin kamfanin Helin International da jami’an gwamnatin Amurka suka kaddamar ne ya bada damar gano hannun kamfanin OKI TRADING dake sahun kamfanonin da kasar Amurka ke bai wa odar kaya a wannan badakala ta tonne 2500 na uranium da kamfanin AREVA da gwamnatin Nijer suka sayar ta barauniyar hanya a Dubai a 2011, inda bayanai ke nuna yadda aka karkasa million 101 na dolar a tsakanin wadanda suka taka rawa aka ci nasara a wannan boyayyiyar harkalla inji jaridar EVENEMENT ta kasar Faransa da ta wallafa wannan labari.

Saurari cikakken rahoton Souley Mummuni Barma cikin sauti:

FARFADO DA BADAKALAR URANIUM GATE.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG