A Karon Farko, Tsohon Shugaba Issoufou Ya Yi Allah-wadai Da Juyin Mulkin Nijar

TSOHON SHUGABA MUHAMMADOU ISSOUFOU

Tsohon shugaban kasar a wannan wasika mai shafuka biyu ya jaddada cewa yana Allah-wadai da juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023 a kasar.

A karon farko dai tsohon shugaban na Nijar ya yi Allah wa da juyin mulkin da Janar Abdourahamane Tiani ya jagoranta a ranar 26 Yulin 2023.

Shugaba Issoufou Mahamadou a wata wasika da ke matsayin martani ga wacce gidauniyar Mo Ibrahim ta tura masa don jin yadda aka yi bai taba yin Allah-wadai da juyin mulkin da aka yi wa shugaba Mohamed Bazoum ba ya bayyana cewa tun a ranar 30 ga watan Yulin 2023 a shafinsa na X ya yi tir da halin da aka tusunduma Nijar ta hanyar amfani da kalmomin da suka dace da yanayin da ake ciki a wancan lokaci.

Asali ma ya bi hanyoyi da dama don ganin an mayar da Bazoum kan kujerarsa, amma barazanar amfani da karfin soja da kungiyar ECOWAS ta ayyana ta haddasa cikas wa abin da ya sa gaba in ji shi.

Ghousmane AbdoulMoumouni wani na hannun daman Issoufou Mahamadou na cewa tun can farko ba su da shakka game da yadda tsohon shugaban kasar ya yi imani da dimokradiya a matsayin mulki mafi cancanta ga al’umma.

Tsohon shugaban kasar a wannan wasika mai shafuka biyu ya jaddada cewa yana Allah-wadai da juyin mulkin 26 ga watan Yulin 2023 a kasar, haka kuma bai yarda da a yi amfani da karfi ba musamman daga ketare domin mataki ne da ka iya rura wutar rikici ya kuma ta da hankalin kasa.

Sai dai da yake bayyana ra’ayinsa a kan wannan matsayi Tchanga Tchaloumbo wani makusancin shugaba Bazoum ya ce bai gamsu da bayanan na shugaba Issoufou ba.

Dambarwa kan rawar da ake hasashen tsohon shugaban na kasar ya taka ko akasin haka a juyin mulkin da Janar Abdourahamane Tiani ya jagoranta wani abu ne da wasu ‘yan kasa ke ganin ba zai canza koma ba a game da tafiyar da sojojin majalissar CNSP suka sha nanata cewa magana ce ta dora kasa kan sabuwar turba.

Tsohon shugaban Issoufou Mahamadou ya karbi lambar yabo daga gidauniyar Mo Ibrahim a 2021 bayan kammala shekaru 10.

Gidauniyar ta saka shi a jerin gwarazan dimokradiya, to amma zarge-zargen da aka yi ta yi dangane da rawar da ake hasashen ya taka wajen kifar da gwamnatin farar hula ya sa gidauniyar aika masa wasika domin ta ji gaskiyar lamari daga gare shi.

Saurari ciakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

A Karon Farko, Tsohon Shugaba Issoufou Ya Yi Allah-wadai Da Juyin Mulkin Nijar