Tsohon Ministan Babban Birnin Tarayyar Najeriya, Abuja, Laftanar Janar Jeremiah Timbut Useni ya rasu a ranar Alhamis, 23 ga watan Janairu, 2025, yana da shekaru 82, bayan doguwar jinya.
A wata sanarwa da ya fitar a Jos, Gwamnan jahar Filato, Caleb Mutfwang ya bayyana rasuwar Janar Useni a matsayin babban rashi ba ga iyalansa kadai ba, har ma da sojojin Najeriya, jihar Filato, da ma kasa baki daya.
Gwamnan ya bayyana kyakkyawan jagoranci na Janar Useni da jajircewarsa wajen yin aiki, wanda ya bar tarihi a fagen tsaro da siyasar Najeriya.
Gwamnan yace za a iya tunawa da irin namijin kokarin da Janar Useni ya yi na inganta zaman lafiya da tsaro musamman a Arewacin Najeriya da Jihar Filato.
Gwamna Mutfwang ya ba da labarin irin rawar da marigayi Janar din ya taka, wanda ya yi wa Najeriya hidima da ayyuka daban-daban, ciki har da ministan sufuri, da kuma ministan babban birnin tarayya Abuja.
Bayan ya yi ritaya daga aikin soja, Janar Useni ya koma siyasa, inda ya ci gaba da yi wa kasa hidima.
Ya taba zama mataimakin shugaban jam’iyyar All Nigeria Peoples Party (ANPP) kuma an zabe shi Sanata mai wakiltar Filato ta Kudu a shekarar 2015 a karkashin jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP).
Gwamnan ya yabawa rayuwar Janar Useni na sadaukar da kai, inda ya yi nuni da irin gudunmawar da ya bayar a bangaren soji da siyasa da kuma al’ummarsa.
Ya kuma jaddada cewa halin Janar din na tausayi, kyautatawa, karamci, da sadaukar da kai ga rayuwar mutane za su dore a rayuwar wadanda ya shafa.