Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Jana'izar Tsohon Firai Ministan Nijar Hama Amadou


Jana'izar Hama Amadou
Jana'izar Hama Amadou

Rasuwar Hama Amadou da ke matsayin tamkar wani abin ba zata ta matukar girgiza jama’a inda hatta ‘yan siyasar da suka sha karawa da shi a fagen siyasa sun nuna alhini kan mutuwarsa, suna masu kwatanta abin a matsayin babbar asara ga kasa.

Yau aka yi jana’izar tsohon fira ministan Nijer Hama Amadou wanda ya rasu a cikin daren Laraba a birnin Yamai.

An gabatar da gawar mamacin a fadar shugaban kasar ta Nijar inda hukumomi da jama’a suka yi masa bankwanan karshe da nufin karrama tsohon fira ministan da ya sadaukar da kansa a aiyukan kasa a tsawon rayuwarsa kafin a fice da shi zuwa kauyensa na haihuwa wato Youri inda aka bizne shi.

Jana'izar Hama Amodou
Jana'izar Hama Amodou

Janar Abdourahamane Tiani ne ya jagoranci wannan taron addu’o'i da bankwanan karshe da ya sami halartar mukarraban gwamnatinsa da tsofaffin shugaban kasa Mahaman Ousman da Salou Djibo da tsohon kakakin majalissar dokokin kasa Seini Oumarou da manyan jiga jigai daga bangarorin siyasa iyalai da dangin mamacin.

Janar Abdourahamane Tiani
Janar Abdourahamane Tiani

Mai jawabin bankwana na cewa "ka tafi a dai dai lokacin da kasarmu ke matukar bukatar hazakarka da sanin makamar aiki da lakantar sha’anin tafiyar da lamuran mulki da ka iya zama babbar gudunmowa a gwagwamayar neman cikakken ‘yancin kasa. Sai dai kash kiran ubangiji ba ya jira.

Jana'izar Hama Amadou
Jana'izar Hama Amadou
Mahalarta jana'izar Hama Amadou
Mahalarta jana'izar Hama Amadou

Tsohon fira Hama Amadou ya tsaya takarar shugabanci kasar a zaben 2011 da 2016 ya kuma yi yunkurin shiga fafatawar a 2020 sai dai hakan ba ta samu ba bayan da kotun tsarin mulkin kasa ta yi watsi da takadunsa a sakamakon hukuncin da ya hau kansa a yayin shari’ar badakalar safarar jarirai, laifin da ya sha nanata cewa bai aikata ba.

Fitaccen dan siyasar ya rasu a wani lokacin da ake kokarin dora kasa kan wata sabuwar turbar ci gaba. wani mataimakinsa a zamanin da suka yi lokaci a jam’iyar MNSD da jam’iyarsa ta Moden Lumana Alhaji Sala Habi na cewa rashin wannan dan taliki gibi ne babba.

Jana'izar Hama Amadou
Jana'izar Hama Amadou

Bayan addu’oi da jawabin bankwanan karshe an yi wa gawar Hama Amadou rakiya zuwa kauyensa wato Youri dake a tazarar km 34 a kudu maso gabsacin Yamai inda aka bizne shi.

Jana'izar Hama Amadou
Jana'izar Hama Amadou

Rasuwar Hama Amadou da ke matsayin tamkar wani abin ba zata ta matukar girgiza jama’a inda hatta ‘yan siyasar da suka sha karawa da shi a fagen siyasa sun nuna alhini kan mutuwarsa, suna masu kwatanta abin a matsayin babbar asara ga kasa.

Saurari rahoton SouleyMoumouni Barma:

An Yi Jana'izar Tsohon Firai Ministan Nijar Hama Amadou
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG