Tsohon Ma'aikacin Google Da Facebook Ya Gano Wasu Hanyoyi

Wani tsohon ma’aikacin kamfanin Google da Facebook ya kaddamar da wani shiri na miliyoyin daloli domin rage illar kafofin sadarwa bayan da ya gano gaskiyar lamarin.

Shirin da aka yiwa lakabi da 'The Truth About Tech' wato 'gaskiya akan kamiyya da fasaha' na son baiwa kananan yara kariya wajen yin amfani da wayoyin zamani, da kuma samar da hanyar rage shakuwa ga yanar gizo.

Shirin zai samar da kayayyakin koyarwa ga makarantu 55,000 a fadin Amurka, a wani yunkuri na bayyana hadarin kafofin sadarwa.

Wani bangare na shirin kuma zai mayar da hankali wajen yin tallace-tallace da kudadenta ya kai har dala miliyan $50, domin nuna illolin yin amfanin da kafofin sadarwa da ya wuce kima, wanda ke haddasa cutar damuwa.

Akwai wasu dokoki biyu da shirin zai mayar da hankali kan rajin ganin an samar da su. Hanyar farko da zai bi itace samar da wani nazari kan yadda kayyayakin fasaha ke shafar lafiyar kananan yara. Hanya ta biyu kuma itace samar da doka da zata kayyade yin amfani da yanar gizo ga kananan yara.

Your browser doesn’t support HTML5

Tsohon Ma'aikacin Google Da Facebook Ya Gano Wasu Hanyoyi - 1'18"