Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya bayyana muhimmancin daukan matakan bai-daya tsakanin gwamnatocin jihohin arewacin Najeriya da hadin gwiwar gwamnatin tarayya domin magance matasalolin tsaro da suka ki ci suka ki cinyewa a yankin.
Bello Matawalle wanda ya tabo batutuwa daban-daban ya kuma bukaci shugabannin arewa su mayar da hankali kan ababen da suke damun al’umma a maimakon siyasa kawai.
Har yanzu dai gwamna Nasiru El-Rufai na jihar Kaduna na ci gaba da jaddada matsayinsa na rashin amincewa da yin sulhu da ‘yan bindigan da ke ci gaba da addabar al’umman yankin arewa maso yamma a Najeriya.
Yanzu dai ‘yan kasa zasu zura ido su ga yadda masu ruwa da tsaki za suyi da shawarar ta gwamna Matawalle.
Saurari rahoto cikin sauti daga Halima Abdulrauf:
Your browser doesn’t support HTML5