Tsaro: Bazoum Ya Gana Da Shugaban Dakarun Faransa

Bazoum Mohamed, Shugaban Kasar Jamhuriyar Nijar

Shugaban kasar Nijar Bazoum Mohamed, ya gana da sabon kwamandan rundunar  Barkhane mai sansani a yankin Sahel inda suka tattauna akan batutuwan da suka shafi yanayin tsaron da ake ciki a  kasashen yankin Sahel.

Wannan ganawa ta Mohamed Bazoum da kwamandan rundunar Barkhane ta kasar Faransa General Marc Conruyt, na gudana ne a wani lokacin da al’amuran tsaro ke kara tabarbarewa a kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso, lamarin da ya sa tattaunwarsu take da muhimmanci a wannan lokacin.

General Marc Conruyt ya ce sun tattauna ne akan yanayin da ake ciki baki daya a yankin Sahel da Sahara, haka kuma sun taba batun hare-haren da aka kai wa dakarun Nijar a baya-bayan nan.

Sannan suka yi nazarin matakan da ya kamata a dauka domin tunkarar wannan matsala a nan gaba.

Tuni dai masu sharhi akan sha’anin tsaro suka fara bayyana matsayinsu a game da tasirin wannan ganawa dangane da yakin da ake gwabzawa da ‘yan ta’adda a yankin Sahel.

A cewar Moustapha Abdoulaye, kwarare a fannin tsaro, mayar da hankali wajen ayyukan inganta rayuwar al’umomin yankunan dake fama da rikici, ita ce hanya mafi fa’ida wajen neman zaman lafiya mai dorewa a maimakon bai wa makamai fifiko.

A shekarar 2012 ne kasar Faransa ta kafa sansani mai kunshe da sojoji 3,500 da nufin tunkarar kungiyoyin ta’addancin da suka mamaye Arewacin kasar Mali.

La’akari da yaduwar aiyyukan wadanan kungiyoy izuwa Nijar da Burkina Faso ya sa gwamnatocinsu fadada ayyukan rundunar ta Barkhane, domin sintiri akan iyakokin kasashen uku.

Sai wasu dubban sojojin rundunar hadin gwiwar G5 Sahel da wasu dakaru 1,200 da Chadi ta aika a wannan yanki.

Saurari rahoton Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

Tsaro: Bazoum Ya Gana Da Shugaban Dakarun Faransa