An bayyana sunayen wadanda shugaban ya gatanta ne a sanarwar da aka fitar fadar White House da sanyin safiyar yau Laraba, sa’o’i kadan kafin wa’adin mulkinsa ya kare.
Afuwar dai ta hada da tsohon shugaban yakin neman zaben Trump, kuma babban mai bashi shawara, Steven Bannon, wanda aka tuhuma da damfarar dubban mutane da suka bada kudaden su domin aikin gina katanga a tsakanin iyakar kudancin Amurka.
Masu gabatar da kara sun zargi Bannon da yin amfani da sama da dala miliyan daya don biyan jami’an yakin neman zaben su da yiwa kansa hidima.
Trump ya sauya hukunci da aka yankewa tsohon magajin garin Detroit, Kwame Kilpatrick, wanda ya ke zaman gidan yari na sama da shekara 20 saboda amfani da mukaminsa a matsayin zababben shugaba da aka kama da laifin cin hanci da rashawa.
Haka kuma shugaban kasar ya yi afuwa ga Dwayne Carter Jr., mawakin gambarar nan da aka fi sani da Lil Wayne wanda ya amsa laifin mallakar makamai.
Sai dai kamar yadda aka yi tunani, Trump bai yiwa kansa ko iyalinsa ko kuma fitattaccen lauyansa kuma amininsa Rudy giuliani.