“Za mu cigaba da karrama tsoffin sojojinmu,” Trump ya bayyana hakan ne jiya Litinin da safe a wajen bude bikin fareti karo na 100 da ake yi duk shekara.
Trump ya kuma bayyana irin nasarorin da gwamnatinsa ta samu, wanda binciken yuwuwar tsige shi ya cigaba da mamayewa a majalisar wakilai mai rinjayen ‘yan jam’iyyar Demokrat.
A lokacin da yake bada misalin samamen da dakarun Amurka na musamman suka kai a watan da ya gabata akan shugaban kungiyar IS, Trump ya ce, “al-Baghdadi ya mutu. Sannan mataimakinsa na biyu shima ya mutu kuma mun saka ido akan na uku mafi girma. Karshen ta'addancinsa ya zo, kuma makiyanmu suna gudu cikin yanayin tsoro sosai.
A ranar 31 ga watan Oktoban data gabata ne dai kungiyar ‘yan ta’addan ta tabbatar da mutuwar dadadden shugabanta, Abubakar al-Baghdadi, kuma ta bayyana wanda ya maye gurbinsa mai suna Abu Ibrahim al-Hashimi al-Qurayshi.