Trump Ya Shawarci Birtaniya Ta Kai Karar Kungiyar Tarayyar Turai

Shugaban Amurka Donald Trump da Firai Ministar Birtaniya Theresa May

Shugaban Amurka Donald Trump ya shawarci Firai Ministar kasar Birtaniya Theresa May ta kai karar Kungiyar Tarayyar Turai turai maimakon tattaunawa da kungiyar, a shirin ficewar kasar daga kungiyar.

Theresa May ta shaidawa tashar talabijin ta BBC cewa, ya gaya min in kai karar Kungiyar Tarayyar Turai, in kai kararsu kada in tattauna da su”.

Bayanin shawarar da Trump ya bada ya kawo karshen kila-wa-kala da aka yi na tsawon kwanaki game da shawarar da shugaban na Amurka ya ba Firai ministar.

Makon jiya Trump ya fada a hirarshi da jaridar The Sun cewa, ya ba May shawara, sai dai bata yi amfani da shawarar tasa ba.

Trump yace “da nine da ba haka zan yi ba. Na gayawa Theresa May abinda ya kamata tayi amma bata yarda ba, bata saurareni ba. Ta gwammace tabi ta wata hanya dabam.

Trump bai bayyana shawarar da ya ba May ba a taron manema labarin na hadin guiwa da suka yi da ita ranar Jumma’a, sai dai yace, ina tsammani taga shawarar tana da nauyi sosai.