Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Shiga Rudanin Siyasa Da Zanga-zanga A Birtaniya


Masu zanga zangar kin amincewa da ziyarar shugaba Trump zuwa London
Masu zanga zangar kin amincewa da ziyarar shugaba Trump zuwa London

Kamar yadda mazauna birnin London suka sha alwashi da isar shugaban Amurka jama'ar garin suka fantsama cikin zanga zangar kin jinin shugaban Amurka Donald Trump

Birnin London da ya shiga rudanin siyasa da zanga zanga da aka yi ta yi akan tituna saboda Donald Trump, na karban bakuncin shugaban na Amurka wanda ya isa birnin a jiya Alhamis.

Wannan ita ziyararsa ta farko a kasar ta Birtaniya, tun bayan da ya hau karagar mulki kusan watannin 18 da suka gabata.

Gabanin isarsa Birtaniyar, shugaba Trump ya kwatanta kasar a matsayin “wuri da ya dau dumi.”

Trump da mai-dakinsa Melania, sun samu tarbar ma’aikatan ofishin jakadancin Amurka da ke Birtaniya.

Ziyarar ta Trump da mai-dakinsa, na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Firai Minista Theresa May take fuskantar kalubale, bayan da Ministan harkokin wajenta Boris Johnson da wasu jami’an gwamnatin, suka yi murabus a wannan mako, a wani mataki na nuna bore kan wani sassauci da Birtaniyan ke sun dauka kan shirinta na ficewa daga kungiyar tarayyar turai.

Shugaba Trump ya yi fatan Amurka da Birtaniya za su cimma matsaya ta fuskar cinikayya.

Wannan kuma wani batu ne da Trump ya samu damar tattaunawa da Firai minister May, yayin wata liyafar ban-girma da aka sirya musu, wacce suka halarta tare da mai-dakinsa, karkashin jagorancin May a dadaddiyar Fadar Blenheim da aka gina tun a karni na 17, wacce ke da tazarar tafiyar kilomita 100, daga arewa maso yammacin London.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG