Shugaban Amurka Donald Trump jiya Jumma'a ya bayyana dangantakar Amurka da Burtaniya a halin yanzu a matsayin wacce ke da muhimmanci fiye da yadda ya taba faruwa a tarihi, ya na mai karyata rahotannin da ke nuni cewa dangantakar kasashen ta dada tsami sanadiyyar wasu kalamansa da aka buga a daya daga jaridun da su ka fi fice a kasar.
Trump, wanda ke tsaye ganga da Firaministan Burtaniya a harabar rukunin gidajenta na Chequers, ya kare kalaman nasa da ke cikin hirar da jaridar ta yi da shi, kalaman da wasu ke ganin ka iya gurgunta tasirin Firaminista Theresa May.
"Jaridar ba ta fadi wasu abubuwan da na fada game da Firaministyar ba alhalin kuwa na fadi mashahuran abubuwa," abin da Trump ya fada kenan yayin da ya ke kare kansa a tambayar da aka masa kan malamansa na caccakar Firaminitar da Jaridar The Sun ta buga.
Facebook Forum