Tsohon Shugaban Amurka Donald Trump ya isa birnin New York bayan da ya baro gidansa na Florida.
Trump mai shekaru 76, ya sauka ne a katafarefn benensan nan da ake kira Trump Tower da ke birnin na New York.
Zai kuma mika kansa ga hukumomin yankin Manhattan a New York a ranar Talata domin fuskantar tuhume-tuhume kan zargin wasu laifuka da ya aikata.
Tsohon shugaban na Amurka ya hawo jirginsa na kansa ne zuwa birnin New York mai dauke da sunansa da manyan haruffa 'TRUMP' a jiki, wanda kafafen yada labarai suka yi ta bibiyar shi har zuwa birnin.
A makon da ya gabata masu taimakawa alkali wajen yanke hukunci suka ce Trump ya karya doka.
Trump zai zamanto tsohon shugaban Amurka na farko da za a tuhuma da laifi, lamarin da ba a taba gani ba a tarihin kasar.
Jami’an tsaron sun kara tsaurara matakan tsaro a birnin na New York domin dakile duk wata tashin-tashina da ka iya tasowa.
Hakan na faruwa ne yayin da rahotanni ke nuni da cewa dumbin magoya bayansa na dunguma zuwa birnin lamarin da ya sa hukumomin tsaro suka yi ta yin kashedi.
“Yayin da muke da masaniyar cewa akwai wasu masu ta-da zaune tsaye da ke shirin zuwa wannan birni namu a gobe (Talata) sakonmu ba shi da wata sarkakiya: ku kasance masu nutsuwa. Birnin New York gidanmu ne.” In ji Magajin Gari New York Eric Adams.
Ko da yake ba a fitar da tuhume-tuhumen da ake yi wa Trump a hukumance ba, amma bayanai sun yi nuni da cewa batun na da alaka da wasu kudaden toshiyar baki da ake zargin ya biya mai fina-finan batsa Stormy Daniels don ta yi shiru da bakinta kan wata mu’amulla da suka yi kafin ya zama shugaban kasa a 2016.
Karkashin wannan tuhuma ana zargin Trump ya ba da bayanan karya kan kudaden da ya kashe kan harkokin kasuwancinsa.
Trump ya sha musanta dukkan tuhume-tuhumen da ake masa, sannan ‘yan Republican da shi kansa Trump sun kwatanta wannan shari’a a matsayin bi-ta-da kullin siyasa.
Democrat a nasu bangaren sun ce shari’ar ta nuna cewa babu wanda ya fi karfin doka a Amurka.