Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana goyon bayan yunkurin sake karfafa matakan binciken masu son sayen bindigogi, biyo bayan harbin da ya kashe mutane 17 a wata makarantar sakandire ta jihar Florida, a cewar fadar White House jiya Litinin.
Goyon bayan Trump na zuwa ne daidai lokacin da ake ta kiran samar da kudurin doka da zata rage yawan harbi.
A wani binciken jin ra’ayin jama’a da jaridar Washington Post da gidan talabijin na ABC News suka fitar da yammacin jiya Litinin, na nuni da cewa kashi 86 na mutanen da suka ce su ‘yan jam’iyyar Democrats ne sunce dokar kayyade bindiga zata iya hana harbin da ya faru na Florida, yayin da kashi 67 na ‘yan jam’iyyar Republican ke ganin dokar bindiga ba zata iya hana faruwar irin wannan harbi ba.
Sama da kashi uku na ‘yan jam’iyyun biyu sunce tantance hankalin masu sayen bindiga da kuma baiwa masu tabin hankali kulawa zai iya kawar da faruwar iftila’in.
Kashi 77 na duk mutanen da suka bada ra’yin na su sun amince cewa ‘yan Majalisun Amurka basa ‘daukar matakan da suka kamata wajen hana faruwar yin harbi, yayin da kashi 62 ke cewa Trump baya yin abin da ya kamata.