Trump Ya Bada Dala 400 Ga Marasa Aikin Yi Sakamakon Corona

Shugaba Trump

Shugaban Amurka Donald Trump a jiya Asabar ya bada amincewar sa ga ci gaba da tsarinn nan da ya zo karshe, na bada tallafin ga miliyoyin Amurkawa da suka rasa ayyukan su a lokacin barkewar annobar coronavirus kana ya dakatar harajin albashi.

Amincewar nasa zuwa bayan tattaunawa da majalisun kasar a kan fito da sabon tsarin tallafin tattalin arziki.

Amurka mai kusan mutum miliyan biyar da aka tabbatar da sun kamu da coronavirus kana wasu dubu 162 suka mutu da cutar ya zuwa jiya Asabar, shugaba Trump ya amince da bada tallafin rashin aikin da ya kai dala dari hudu a kowane mako, adadin da ya gaza da kashi daya cikin uku a kan dala dari shida da ake badawa a baya. Majalisun sun tabbatar da da ranar daya ga watan Agusta ne ranar da shirin zai zo karshe kana tattaunawa a kan ci gaba da tsarin ta huskanci matsala a ranar Juma’a, inda fadar White House da Democrat suka raba gari a wannan batun.

"Wannan shine kudin da suke bukata, shine kudin da suke so, wannan ne zai basu kwarin gwiwar komawa bakin aiki, inji Trump yayin da yake tsokaci a kan dan taimakon rashin aikin a wani taron manema labarai a jihar New Jersey.

A halin da ake ciki shugaban masu rinjayi a majalisar dattawa Mitch McConnell ya fada a wata sanarwa a jiya Asabar cewa Amurkawa da basu da aikin yi na bukatar taimako a yanzu. Ya ce tun da yake ;yan Democrat sun lalata zaman tattaunawar da bukatu masu yawa wanda ba zai taimakawa mutanen da basu da aikin yi, ya ce yana goyon bayan shugaba Trump ya yi amfani duk wata hanya da yake da ita ya bada tallafin da ma wasu taimako da mutane ke bukata.