Mai Yiwuwa Ba Abin Da Taronmu Da Putin Zai Tabuka - Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump a lokacin da ya isa filin tashin jirage na Helsinki a jiya Lahadi, Yuli 15 2018

Shugaba Trump na Amurka ya nuna shakku kan yiwuwar samun wani kyakkyawan sakamako a taron kolin da za su yi da takwaran aikinsa na Rasha Vladimir Putin a kasar Finland.

Sa’o’i gabannin taron kolin da zai yi da shugaban Rasha Vladimir Putin, shugaban Amurka Donald Trump yana nuna alamun sai ta yiwu babu abin da taron zai tabuka.

Haka nan ya yi matukar sukar lamirin wadanda ake gani bisa al’ada kawayen Amurka ne.

A hirar da tashar talabijin ta CBS ta yi da Mr. Trump, Ya ce kungiyar tarayyar turai abokiyar gaba ko hamayyar Amurka ce.

Ya ce sai ta yiwu baka kallonsa a haka, amma abokan gaba ne.” Haka nan Trump ya ce Rasha ma “a wasu fannoni abokar gaba ce.”

Shugaban Majalisar Turai Donald Tusk, ya mai da martani cikin sauri ta shafin Twitter.

“Amurka da Turai kawaye ne sosai. Kuma duka wanda yake yada labarin cewa abokan gaba ko hamayya ne, yana yada kariya.”

Za a yi ganawar ce kwanaki uku bayan da lauya na musamma Robert Mueller ya gabatar da tuhuma kan jami’an leken asirin Rasha guda goma 12 da zargin su da laifin yin shisshigi a zaben shugaban Amurka 2016 da ake ganin ya taimaka wajen dora Mr Trump akan karagar mulki.