Shugaban Amurka Donald Trump ya ce labudda zai tinkara Shugaban Rasha Vladimir Putin, kan katsalandan din da ake zargin Rasha da yi a zaben Shugaban kasar Amurka na 2016, wanda don haka ma aka kafa wani kwamitin binciken, kwamitin da Trump ke watsi da shi a matsayin bita da kullin siyasa.
"Ina ganin wannan al'amari ya yi illa ga kasarmu," a cewar Trump a wani taron manema labarai tun a Burtaniya bayan ganawarsa da Firaministar Burtaniyar Theresa May. Ya kara da cewa, "Wannan ya yi matukar illa ga dangantakarmu da Rasha. Ina ganin akwai damar kulla kyakkyawar dangantaka da Rasha da kuma yiwuwar hulda mai kyau da Shugaba Putin. Ina fatan haka."
Trump ya ce bai ma sa ran al'amarin zai zo da sauki idan ya tinkari Putin kan wannan batun; ya nuna cewa Putin zai cigaba da musantawa ne kawai.
"Ban tsammanin zai ce 'e,' na aikata, na aikata, ko ba ku gane ba," a cewar Trump. Ya kara da cewa, "Ba na tsammanin tuhumar da zan yi ma Putin za ta haifar da abin da ya faru dinnan bayan tuhumar Perry Mason, wato inda aka ga saukin amsa laifi; to amma kuma sanin gaibu sai Allah."
Facebook Forum