Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Yi Nasara a Taron NATO


Shugaba Donald Trump ya ce ya samu tabbacin shugabannin kasashen Turai akan cewa za su kara kudaden da suke kashewa wajen samar da tsaro

Bayan shugaban na Amurka ya share kwanaki yana kukan cewa duk kasashen sun bar dawainiyar kashe kudaden akan Amurka kawai.

Trump yace yanzu kasashen Turan, wadanda a jiya yace kashi 2 cikin 100 na kasafin kudadensu kawai suke bayarwa a matsayin tarbacce ga harkar tsaron, yanzu za su kara zuwa kashi 4 cikin 100 kafin shekarar 2024.

Haka kuma Trump yayi barazanar cewa zai fitar da Amurka daga Rundunar Tsaron ta Turai, watau NATO, idan ba’ayi wa Amurka adalaci ba wajen daukar nauyinta, inda yace Amurka ce ke samarda tsakanin kashi 70 zuwa kashi 90 cikin 100 na kudaden gudanarda ita.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG