Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce sun tattauna da takwaran aikinsa na Rasha, Vladimir Putin kan batutuwa da dama wadanda za su taimakawa kasashen biyu a nan gaba.
“Ina da muradin ganin abubuwa masu alfanu sun faru da Amurka da Rasha.” In ji Trump a lokacin ganawarsa ta ido-da-ido ta farko da ya yi da Putin a hukumance.
Wannan tattaunawa, ita tafi mamaye batutuwan da za a yi dubi a kansu a taron kasashe na G20 da suka fi karfin tattalin arziki a duniya a birnin Hamburg dake Jamus.
Har ila jama’a da dama na ganin tattaunawar karkacacciya ce, lura da cewa Trump sabon-shiga ne a harkar diplomasiyyar duniya idan aka kwatanta da Putin wanda tsohon ma’aikacin kungiyar leken asiri ta KGB ne, wanda ya shahara wajen amfani da dabarar jefa fargaba a zukatan wadanda zai tattauna da su.
Putin ya karbi ragamar mulkin Kremlin ne bayan wani abu da wasu ke mai kallon a matsayin juyin mulki shekaru 17 da suka gabata
Masu sa ido kan ala’muran yau da kullum, sun fi maida hankali kan yadda wannan tattaunawa ta kasance, lura da cewa an samu tsatsamar dangantaka tsakanin tsohon shugaba Barack Obama a da, abinda Trump ya ce yana so ya gyara.