Dan takarar shugaban kasa a karkashin jami’iyar Republican a nan Amurka Donald Trump, ya bukaci da a samar da mai shigar da kara na musamman dake zaman kansa, wanda zai binciki gidauniyar Hillary da mijinta Bill Clinton, domin a cewarsa, ba za a iya dogaro da hukumar binciken manyan laifuka ba ta FBI ba wajen gudanar da wannan aiki.
WASHINGTON DC —
Trump dai ya yi amfani da lokacin yakin neman zabensa a Akron da ke jihar Ohio, inda ya nuna matukar kaduwarsa kan irin abin rashin gaskiya da ya zargi Hillary ta aikata.
Wasu masu adawa da Clinton a jami’iyar Republican sun ce masu taimakwa gidauniyar sun yi amfani da wannan dama, inda suka amfana da mukamin Clinton ko kuma wasu manyan mataimakanta, a lokacin da take Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka.
Clinton dai ta jima ta na musanta wannan zargin.
Yayin da wasu sabbin sakonnin email da aka fitar, suka nuna cewa an nemi alfarma daga hannun wasu mataimakan Clinton, babu wata hujja da ta nuna ko an ba da alfarmar ko kuma Clinton na da hannu a ciki.