Hilary dai tana son tayi anfani da wannan damar ce biyo bayan cewar abokin karawar ta na jamiyyar Republican Donald Trump yace ayi mata tujara.
Clinton wadda tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka ce ta samar da wani shafin yanar gizo mai take togetherforamerica.com.
Ta samar da wannan shafinne da zummar samun Karin sunayen masu jefa kuria, Shafin na cewa ita ce ta fahinci yanayin al’ummar Amurka mai sarkakiyya da yanayin duniya mai cike da rudani, kana tana da karfin zuciyar zamowa shugabar kasa da babbar kwamandar askarawan Amurka abinda Donald Trump baya dashi.
Tayi wannan rokonne bayan sa’oi kadan da Trump ya shaidawa taron masu jefa kuria a ranar talata cewa muddin Clinton ta zamo shugabar kasar to ba shakka zata yiwa dokar kasa gyaran fuskar da zai hana mutane mallakar bindiga domin su kare kansu.
Yace batun mallakar bindiga a halin yanzu yana bisa hadari musammam a wannan lokacin zaben.