Trump Na Shirin Yanke Shawara Kan Yarjejeniyar Nukiliyar Iran

Shugaba Trump

Shugaba Trump ya dade yana caccakar wannan yarjejeniyar yayinda kasashen Turai ke yin kiran ya bar Amurka a cikin yarjejeniyar.

A yau ne ake sa ran cewa shugaban Amurka Donald Trump zai yanke shawara akan ko Amurka zata ci gaba da kasancewa a cikin yarjejeniyar nan da manyan kasashen duniya suka kulla da Iran dangane da makomar shirinta na kera makaman nukiliya, ko kuma zai fitar da Amurka daga yarjejeniyar.

Daman shugaban ya dibarwa kansa wa’adi har zuwa ranar Asabar don yanke wannan shawarar da har ila yau ta shafi matakan horaswar da manyan kasashen Turai da suka hada da ita Amurka din, da Ingila, Faransa, Rasha da Jamus suka dauka akan Iran don matsa mata lambar tayi watsi da duk wani shirinta na neman makaman kare dangi.

Tuni dai Trump ya sanar a shafinsa na Twitter cewa da misalin karfe 2 na rana, agogon Amurka, (misalin karfe 7 na yamma agogon Nigeria da Nijar) zai sanar da duniya matsayar da ya cimma.