Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gawayi, Ruwan Sama Sun Halaka Mutane a Taraba


Wasu masu sana'ar sayar da gawayi a kasra Somalia
Wasu masu sana'ar sayar da gawayi a kasra Somalia

Rahotanni daga jihar Taraba arewa maso gabshin Najeriya na cewa mutum uku sun mutu a cikin daki sakamakon shakar hayakin gawayi a Gembu,haka nan kuma wasu sun rasa rayukansu a Jalingo fadar jihar biyo bayan ruguzowar turakun sadarwa na kamfanonin sadarwa wato mas, sakamakon ruwa da aka yi kamar da bakin kwarya.

Kamar yadda bayanai ke nuna abun alhinin ya faru ne a anguwar sabuwar tashar Gembu,na karamar hukumar Sardauna dake jihar Taraba,inda aka samu gawarwakin mutane uku a daki guda, bayan da suka kwanta barci,lamarin da yanzu haka ya jefa jama’a cikin mamaki da ta’aji bi.

Cikin wadanda suka mutum har da wani dattijo dake da kimanin shekaru casa’in (90) a duniya da ‘ya’yansa biyu.

Ana dai kyautata zaton cewa hayakin gawayi ne ya kashe su a daki cikin dare. Abdul Hadi Musa, da ne ga dattijon da ya rasun ya bayyana yadda lamarin ya faru. Ya ce ya kunna ma mahaifinsa gawayi domin dumama dakinsa kamar yadda yake yi masa kullum, sai a wannan lokacin basu bude tag aba.

Shima dai mai anguwan wannan waje da lamarin ya faru wanda bai so a ambaci sunansa ba,ya shawarci jama’a da su kula musamman wajen amfani da gawayin dumama daki,risho ko kuma jannareton bada wuta. A cewarsa hakan ya taba faruwa yayinda wasu suka kunna janareto. Mutum daya ya rasu sanadiyar shakar hayakin kana daya ya sha da kyar.

Kuma wannan abun tashin hankalin na zuwa ne yayin da a Jalingo fadar jihar Taraban, aka samu faduwar turakun sadarwa na antenna,bayan ruwan sama da iskar da aka yi kamar da bakin kwarya,wadanda suka haddasa asarar rayuka da gidaje.

Da yake tsokaci game da abun da ya faru Mr. Julius I.Butu, babban daraktan hukumar kare muhalli ta jihar Taraban,ya gargadi jama’a da suke kulawa da yadda kamfanonin sadarwa ke kafa turakunsu walau a gidaje ko kuma wuraren hada hadar jama’a su dinga kiyayewa.

‘’Abun takaici ne ma yadda jama’a ke nuna halin ko in kula da yadda kamfanonin sadarwa ke kafa turaku a gidaje ko a muhallansu ba tare da samun izinin hukuma ba. Dole a sa ido da kuma bincikawa daga hukuma don kare lafiyar jama’a’’, a cewarsa.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG