Sun fadada ratar dake tsakaninsu da abokan takararsu, a yunkurin samun zama 'yan takarar shugabancin Amurka na jam'iyun Republican da kuma Democrat.
Bayan an kidaya kusan dukkan kuri'u, Trump ya sami gagarumar nasara da kusan kashi 60 cikin dari, idan aka kwatanta da kashi 25 cikin dari, da gwamna John Kasich, na jihar Ohio ya samu, shi kuma sanata Cruz, ya sami kashi 15 cikin dari. yayinda Madam Clinton ta doke senata Bernie Sanders da kashi 57 cikin dari, sanders kuma da ya sami kashi 42 cikin dari.
Bisa dukkan alamu Trump ne zai lashe dukkan wakilai 95 na jihar New York, wanda zai bashi wakilai 835 bayan zaben na jiya Talata. Akwai bukatar wanda zai zama dan takarar jam'iyyar Republican ya sami wakilai 1,237, matakin da ake gani da wuya Donald Trump, ya samu, kamin nan da babban taron jam'iyyar, cikin watan Yuli.
Ita kuma Madam Clinton kamin zaben na jiya Talata, tana da wakilai 1,758, da nasarar da ta samu a New York, yanzu kusan tana da wakilai 1,900, shi kuma senata Sanders, yana da wakilai ko delegates 1,185.
Jam'iyyar Democrat tana bukatar wanda zai yi mata takara ya sami ko ta sami nasarar samun wakilai 2,383 a zabukan share fage da ake yi.