Wasu bayanai da Babban Atoni-Janar din Amurka, William Barr ya fitar a takaice, sun nuna cewa kwamitin Robert Mueller na musamman, ya bayyana cewa, shugaba Donald Trump da kwamitin yakin neman zabensa ko wani da ke da alaka da shi, ba su hada kai da Rasha ba domin a yi katsalandan a zaben shugaban kasar na 2016.
Amma dangane da ko shugaba Trump ya yi kokarin kawo cikas ga binciken da kwamitin na Mueller ke yi, Barr ya bayyana cewa, “rahoton bai dauki matsaya ba, kan ko shugaban ya aikata laifi, sannan kuma bai wanke shi ba.”
A jiya Lahadi, babban Atoni janar din, ya fitar da kanun rahoton na Mueller da aka jima ana jiran sakamakonsa a binciken da aka kwashe watanni 22 ana gudanarwa, kan zargin cewa kwamitin yakin neman zaben Trump ya hada kai da Rasha domin ta taimaka mai.
A jiya Lahadi, Barr ya aikwa da majalisar dokokin Amurka rahoton, bayan da shi ma Mueller ya mika rahoton ga ma’aikatar shari’ar Amurka a ranar Juma’a.