Shugaban Amurka Donald Trump, ya ce China za ta ci gaba da biyan kudaden harajin da aka saka mata nan da zuwa wani lokaci, ko da an cimma wata yarjeniyar kasuwanci.
A cewar Trump, ana samun ci gaba a tattaunawar da ake yi da hukumomin Beijing, inda ya ce nan da wasu ‘yan kwanaki, wakilan Amurka za su tafi China domin ci gaba da tattaunawar.
Sai dai masana tattalin arziki na ganin China ba za ta amince da matsayar ta Amurka ba.
Alkaluma dai sun nuna cewa, adadin kayayyakin da China take shiga da su Amurka, sun ninninka wadanda Amurkan take kai wa China.
Baya ga haka, wannan rashin daidaito a fannin kasuwanci a tsakanin kasashen biyu, shi ya dibi kashi 80 cikin 100 na adadin gibin da Amurka take samu a fannin kasuwancinta da kasashen duniya.
Facebook Forum