Shugaban Amurka Donald Trump, ya yi barazanar zai rufe ma'aikatun gwamnati idan har majalisar dokokin Amurka ba ta ware kudi domin a gina katanga kan iyakar kasar da Mexico ba.
Shugaban na Amurka, ya yi ikirarin cewa tilas 'yan hamayya daga jam'iyyar Democrat su goyi bayansa kan kare kan iyaka da zai kunshi kudi domin gina katanga, da kuma sauye sauye masu tsanani ta fuskar shige da fice.
Sai dai wani bangare na jam'iyyar Republican mai rinjaye, tare da 'yan Democrat wadanda kan su yake hade ne, har sau biyu suka yi watsi da kudurorin shige da fice da shugaban na Amurka yake goyon baya, lamarin da ya auku a baya-bayan nan.
A wani sakon Twitter,Trump ya yi kira ga Amurka ta koma amfani da "shirin shige da fice wanda ya ba da fifiko ga cancanta, yana mai cewa "muna bukatar mutanen kwarai su shigo kasarmu.