Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Maida Gawawwakin Sojin Amurka Daga Koriya


Wani jirgin sojin Amurka ya mayar da akwatuna 55 na gawarwakin da Koriya ta Arewa tace ma'aikatan Amurka ne da aka kashe a yakin Koriya fiye da shekaru 60 da suka wuce.

Jirgin da ya sauka a Koriya ta Kudu a safiyar yau jumma'a, ya samu rakiyar kwararru daga Majalisar Dinkin Duniya da kuma hukumar kare fursunonin yaki POW/MIA.

Dawo da su din da akayi ya soma tabbatar da yarjejeniyar da aka cimma a watan da ya gabata, tsakanin shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong Un da shugaban Amurka Donald Trump a lokacin da suka yi zaman tattaunawa mai dimbin tarihi a kasar Singapore. Trump yayi amfani da shafin sa na Twitter inda ya yi wa Kim godiya bayan da gawarwakin suka sauka a Koriya ta kudu.

Kimanin sojojin Amurka 7,700 ne suka bace a yakin Koriya kuma ana kyautata zaton mafi yawancin gawarwakin har yazu suna Koriya ta Arewa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG