Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai yi jawabi ga kasa baki daya a ranar Talata, 1 ga Oktoba, 2024, da karfe 7 na safe.
Kakakin Tinubu, Bayo Onanuga ne ya bayyana hakan a wata takaitacciyar sanarwa a ranar Litinin.
A ranar Talata 1 ga watan Oktoba Najeriya ta cika shekaru 64 da samun ‘yancin kai.
“Jawabin na daya daga cikin ayyukan tunawa da cika shekaru 64 da samun 'yancin kai na kasa.” In ji Onanuga.
Bisa al’ada, jawabin da shugaban kasa ke gabatarwa kan kunshi bayanai kan halin da kasa ke ciki musamman abubuwan da suka shafi tattalin arzikin kasa.
Najeriya na fuskantar hauhawar farashin kayayyaki tun da aka cire tallafin mai a shekarar 2023 da matsalar tsaro da ta addabi wasu sassan kasar.
A ranar jajiberin cikar Najeriya shekaru 64, babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta yi kira ga Shugaba Tinubu da ya rage kudin man fetur.