ABUJA, NIGERIA - Tafiyar dai za ta kunshi halartar taron kolin Saudiyya da Afirka da kuma taron kasashen Larabawa da Afirka da za a yi a ranakun 10 da 11 ga watan Nuwamban 2023.
Ajuri Ngelale, mai magana da yawun shugaban kasar Najeriya, ya jaddada cewa ajandar shugaba Tinubu a kasar Saudiyya ta kunshi tattaunawa da dama da nufin karfafa alakar tattalin arziki tsakanin kasashen biyu. Yaki da ta'addanci, matsalolin muhalli, da bunkasuwar aikin gona na daga cikin muhimman batutuwan da za’a tattauna.
Ngelale ya bayyana muhimmiyar rawar da Tinubu ke takawa a matsayinsa na shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS) tare da jaddada kudirinsa na bayar da shawarar zurfafa hadin gwiwa a tsakanin yankunan biyu. Tattaunawar za ta kuma shafi inganta harkokin kasuwanci da zuba jari tsakanin Saudiyya da nahiyar Afirka.
Ngelale ya ce "Yayin da yarjejeniyar ciniki 'yanci ta nahiyar Afirka ta fara yin tasiri, shugaba Tinubu yana da sha'awar tabbatar da ganin Najeriya ta kara girman matsayinta a cikin kasuwannin da ke nahiyar. Hukumar Tattalin Arziki ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi hasashen kasuwar za ta haura dala tiriliyan 29 nan da shekarar 2050," in ji Ngelale.
Ziyarar ta shugaba Tinubu a Saudiyya za ta zo dai-dai da wasu muhimman taruka guda biyu, wato taron kolin Saudiyya da Afirka da kuma taron kasashen Larabawa da Afirka.
Na farko dai zai tattauna batutuwa daban-daban da suka shafi hadin gwiwa a fannin tattalin arziki, yayin da na biyu zai mayar da hankali kan raya ababen more rayuwa, ciki har da kafa hanyar zirga-zirgar jiragen kasa mai sauri tsakanin kasashen kungiyar Larabawa da kasashen Tarayyar Afirka.
Ngelale ya kara jaddada yuwuwar Najeriya na yin amfani da matsayinta na kan gaba a nahiyar Afirka, yana mai jaddada fatan karfafa huldar tattalin arziki da huldar kasuwanci da kasashen Larabawa.
Ya bayyana jajircewar da shugaba Tinubu ya yi na bunkasa zuba jari daga ketare da kuma habaka tattalin arzikin kasa, musamman ta hanyar yin cudanya da masu zuba jari da kuma neman saka hannun jari a muhimman sassa na tattalin arzikin Najeriya.
“Muna sa ran samun sakamako mai ma’ana daga wadannan tarurrukan, tare da jaddada alfanun da Najeriya za ta samu a karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu,” in ji Ngelale.
Zamu iya cewa, irin wadannan taruka da damammaki zasu iya baiwa shugaba Tinubu damar kara samun sabbin hanyoyin farfado da tattalin arzikin Najeriya lura da halin da kasar ke ciki a halin yanzu na kalubalen matsin tattalin arziki.
-Yusuf Aminu Yusuf