AGADEZ, NIGER - Mahalarta taron dai sun yi musayar ra’ayoyi akan hanyoyin da za a bi wajen karfafa dangantaka tsakanin bakin haure da al’ummar da suke rayuwa tare da su a Nijar, da kuma matakan shawo kan matsalolin da bakin haure suke fuskanta.
Taron wanda ya kunshi jakadun kasashe tara na Africa ta yamma ciki har da Najeriya da Chadi da sarakunan gargajiya da hukumar dake kula da bakin haure ta Majalisar Dinkin Duniya da gwamnatin Nijar, an gudanar ne domin wayar da su hakkokinsu da kuma sanar dasu dokar kasar da suke ciki don kuma kare hakkokin bakin hauren a matsayinsu na bil adama.
Hukumar kula da bakin haure ta duniya ta bukaci a yi tsari na musan man don ganin cewa an kula da duk wanda ya shigo Nijar kuma an san halin da yake ciki da sanar da jami’an hukumar kulada bakin haure.
Suma ana su bangare sarakunan gargajiya sun yi kira ga kungiyar ECOWAS ko CEDEAO da ta sassauta takunkuman da ta sanyawa Nijar don mayar da bakin haure kasashen su na asali.
Oumarou Ibrahim Oumarou mai martaba sarkin abzin baki da mahalarta taron sun yi na’am da cewar muddun ba a dauki nagartattun matakkai ban a yaki da zaman kashe wando, fatara da talauci da suka yawaita a Nahiyar Africa akwai matukar wuya a magance matsalolin bakin haure.
Saurari cikakken rahoto daga Hamid Mahmud:
Dandalin Mu Tattauna