Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Akufo-Addo Ya Bukaci Majalisar ECOWAS Ta Tattauna Kan Tsawaita Wa'adin Shugaban Kasa


Shugaba Akufo-Addo
Shugaba Akufo-Addo

Shugaban Ghana, Nana Addo Dankwa Akufo-Addo, ya yi kira ga mambobin majalisar ECOWAS da su tattauna kan karin wa'adin shugaban kasa da wasu shugabanni suka yi domin tsawaita zamansu kan karagar mulki, a wani mataki na kaucewa tashin hankali a kasashen yankin.

Shugaba Akufo-Addo ya fadi hakan ne, yayin da yake jawabi wajen bikin bude wani babban taron majalisar dokokin ECOWAS da aka fara ranar Juma’a 29 ga watan Satumba zuwa 7 ga watan Oktoba 2023.

Taken taron shi ne ‘Rawar da Majalisar ECOWAS za ta taka: dangane da kalubalen da ke tattare da sauyin tsarin mulki ba bisa ka’ida ba da kuma iyakance wa’adin shugaban kasa a yammacin Afirka’, wanda majalisar ECOWAS ta shirya a garin Winneba da ke kasar Ghana.

Shugaba Akufo-Addo
Shugaba Akufo-Addo

"Ina kira ga ‘yan majalisar ECOWAS da su yi magana kan karin wa’adin mulkin shugaban kasa da wasu shugabanni suka yi domin karfafa zamansu kan mulki. Wadannan ayyukan suna haifar da rashin jin daɗi a tsakanin jama'a, wanda ke haifar da yanayi mai kyau ga sojojin juyin mulki su gudanar da aikinsu." Shugaba Akufo-Addo ya ce.

Riko da wannan, in ji shugaban, zai tabbatar da cewa ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da dimokuradiyyar kasashenmu, inda ya kamata mu samar da tsarin gudanar da mulki bisa tsarin raba madafun iko.

Shugaba Akufo-Addo
Shugaba Akufo-Addo

"wannan kira ya yi domin yawancin juyin mulki da yawa da suka faru a Afirka, na da alaka da hakan. A Afirka ne za ka samu shugaba na shekaru 40 yana kan mulki, wanda hakan ba daidai ba ne." In ji Mai sharhi kan harkokin siyasa, kuma sakataren jam’iyyar CPP na yankin Ashanti, Issah AbdulHamid.

Sai dai Malam Siba Shakibu, Sakataren jam’iyar PNC, reshen yankin Accra, ya ce ko da yake kiran ya yi daidai, amma da ya dau mataki a lokacin da yake shugaban kungiyar ECOWAS da ya fi.

Ya ce, idan ya yi wannan kira a gaban shugabannin Afirka shi ne mafi dacewa, domin ‘yan majalisan dokoki ba su da karfin ikon hana shugabannin kasashe aiwatar da kudurorinsu.

Shugaba Akufo-Addo
Shugaba Akufo-Addo

Yunus Salahudeen Wakpenjo, mai sharhi kan siyasa da al’amuran yau da kullum, yace wannan kira daga bakin daya daga cikin shugabannin da suke karfin yin hakan, na nuni da cewa, za a iya cimma burin dimokradiya a yankin.

Majalisar ECOWAS na kunshe ne da kujeru 115, inda kowace kasa membobi ke da tabbacin samun mafi karancin kujeru biyar, yayin da sauran kujeru 40 aka raba su bisa yawan al’umar kasa.

Wannan ne karo na biyu da kasar Ghana ta karbi bakuncin wannan taron da ake gudanarwa sau biyu a shekara.

Saurari rahoton Idris Abdullah:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG