Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taron Majalisar Commonwealth Karo na 66 A Birnin Accra


Taron Majalisar Commonwealth Karo na 66 A Birnin Accra, Ghana
Taron Majalisar Commonwealth Karo na 66 A Birnin Accra, Ghana

Shugaban Ghana, Nana Akufo-Addo, ya bukaci ‘yan majalisar kungiyar kasashe renon Ingila da su yi aiki tare, domin kiyaye ka’idojin dimokuradiyya da kimar kungiyar Commonwealth, yayin da ya kaddamar da bude taron majalisar dokokin Commonwealth karo na 66 ga wakilai sama da 500 a birnin Accra, Ghana.

ACCRA, GHANA - Wannan shi ne karo na farko da Ghana ta karbi bakuncin taron majalisar dokokin kasashe renon Ingila (CPA). Yankin CPA na Afirka, daya ne daga cikin yankuna tara na kungiyar, kuma wannan ne karo na 17 da yankin ke gudanar da taron na shekara-shekara.

Taron Majalisar Commonwealth Karo na 66 A Birnin Accra, Ghana
Taron Majalisar Commonwealth Karo na 66 A Birnin Accra, Ghana

Shugaban Ghana, Nana Akufo-Addo, wanda ya gabatar da jawabi na musamman a bukin bude taron mai taken, “Yarjejeniyar Commonwealth Shekaru 10 Nan Gaba: Dabi’u da ka'idojin da majalisar za ta tabbatar," ya ce “Ina kira ga 'yan majalisar Commonwealth da su yi tunani mai zurfi a kan manufar dabi'u da ka'idoji da ke cikin Yarjejeniyar ta Commonwealth, kuma su mai da hankali wurin tattaunawa kan burin kiyaye dimokuradiyyar wannan al'umma mai daraja”

Taron Majalisar Commonwealth Karo na 66 A Birnin Accra, Ghana
Taron Majalisar Commonwealth Karo na 66 A Birnin Accra, Ghana

Ya kara da ce wa “Ina yaba wa Commonwealth saboda jajircewarta na bin doka da oda, al'ummomi masu fa'ida da fahimtar juna, daidaito ga kowa da kuma mutunta muhimman hakkokin bil'adama da 'yancinsu."

Haka kuma shugaba Akufo-Addo ya tabo batun illolin sauyin yanayi, ta’addanci da kuma yawan juyin mulki da suke yi wa dimokradiya barazanar kafuwa a wannan yankin.

Taron Majalisar Commonwealth Karo na 66 A Birnin Accra, Ghana
Taron Majalisar Commonwealth Karo na 66 A Birnin Accra, Ghana

Mai sharhi kan harkokin yau da kullum, Issah Mairago Gibril Abbas, ya ce jawabin shugaba Akufo-Addo na kan gaba, amma sai dai, ‘Idan bera da sata, daddawa ma na da wari’, shugabannin farar hula na da bukatar gudanar da mulki yadda dimokradiya ta gindaya.

Babban Sakataren kungiyar majalisar dokokin commonwealth, Stephen Twigg, ya bayyana farin cikinsa ga karimcin Ghana ga bakin da suka halarci taron.

Ya ce “bari in yi amfani da wannan damar don gode muku duka da kasancewa a nan. Kuma ina yi wa kowa fatan alheri, da gudanar da taro mai tasiri, da fatan an yi taro mai kayatarwa, tare da kuma karimcin da muka riga muka samu daga masu masaukinmu, Ghana. Karimci ne na musamman kuma ina yi muku godiya.”

Taron Majalisar Commonwealth Karo na 66 A Birnin Accra, Ghana
Taron Majalisar Commonwealth Karo na 66 A Birnin Accra, Ghana

Game da taron na bana, mai sharhi kan harkokin kasa da kasa da kuma tsaro, Irbad Ibrahim ya yi tsokaci cewa, lallai kasashen da kasar Burtaniya ta mulka na bukatar su hadu domin taimakawa juna, shi ya sa ake yin bayayya tsakanin kasashen domin daukar bakuncin taron. Kuma kasancewar Ghana mai masaukin baki ya dace, idan aka yi la’akari da ci gaban dimokradiyarta tun 1992 zuwa yanzu babu juyin mulki.

Lokacin Taron Majalisar Commonwealth Karo na 66 A Birnin Accra, Ghana
Lokacin Taron Majalisar Commonwealth Karo na 66 A Birnin Accra, Ghana

Taron zai yi nazari kan batutuwa da dama da suka danganci bita kan barazanar ta'addanci zuwa kason jinsi a Majalisun Dokoki, yaki da talauci kan makamashi da samun ci gaban kasuwanci da tattalin arziki mai dorewa, da tattaunawa da matasa.

Haka kuma za a gudanar wasu tarukan karawa juna sani a gefen taron majalisar commonwealth din; da suka hada da tattaunawa da ‘yan majalisar Commonwealth mata (CWP) da kuma ‘yan majalisar commonwealth da ke fama da larurar nakasa.

Saurari açıkken rahoto daga Idris Abdullah:

An Fara Gudanar Da Taron Majalisar Commonwealth Karo na 66 A Birnin Accra.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG