Tinubu Zai Gabatar Da Karamin Kasafin Kudin Bana Ga Majalisar Kasa

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu (Hoto: Facebook/Bola Tinubu

Nan bada jimawa ba Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai gabatar da karamin kasafin kudin bana ga Majalisar Dokokin Kasar.

A jawabinsa ga zaman hadakar zaurukan majalisun tarayya 2 a yau laraba shugaban kasar yace, “na riga na gabatar muku da tsohon kasafin.”

A nasa martanin, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, yace, “muna godiya, ya mai girma shugaban kasa, muna sa ran karabar karamin kasafin 2024 nan bada jimawa ba.”

Har ila yau, a yayin zaman majalisun na hadin gwiwa wanda ya dace da bikin cikar Tinubu shekara guda akan gadon mulki, shugaban ya tabbatar da taken “Nigeria we hail thee” a matsayin sabon taken Najeriya.

Tinubu ya kara da cewar, “ku kada mana sabon taken najeriya na, “nigeria, we hail thee”. wannan shi ke kara fito da irin hadin kai da bambance-bambancen dake tsakaninmu, dake wakiltar kowane daga cikinmu tare da curewa a wuri daya a matsayin ‘yan uwan juna maza da mata.”

Shugaban kasar ya kuma bukaci dukkanin zaurukan majalisun 2 dasu cigaba da baiwa gwamnatinsa hadin kai tare da yin aiki tare domin gina kasa akan tafarkin cigaba mai dorewa.