Fadar shugaban kasar dai ba ta bayyana abin da Tinubu zai je yi a Faransar ba.
Washington D.C. —
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya tafi Faransa a ranar Litinin a cewar wata sanarwa da kakakinsa Ajuri Ngelale ya fitar.
Ziyarar ta Tinubu na zuwa ne kwanaki biyu bayan da ya dawo daga Equatorial Guinea inda shugaban na Najeriya da takwaran aikinsa Teodoro Obiang Nguema suka amince da rattaba hannu kan yarjeniyoyi a fannin hakar mai da gas da tsaro.
Sai dai ba kamar ziyarar Equatorial Guinea da aka bayyana dalilin tafiyar ba, fadar shugaban kasar ba ta bayyana dalilin zuwan Tinubu kasar ta Faransa ba.
“Shugaban zai dawo kasa bayan ya kammala aiki a kasar ta Faransa.” In ji Ngelale.