Shugaban Najeriya ya nada sabbin shugabannin da za su jagoranci hukumomin tattara bayanan sirri na NIA da hukumar 'yanasandan farin kaya ta DSS.
Wata sanarwa da kakakin Tinubu Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Litinin, ta ce Ambasada Mohammed Mohammed ne sabon shugaban hukumar ta NIA.
Kazalika an nada Mr. Adeola Oluwatosin Ajayi a matsayin sabon Darekta-Janar na hukumar ta DSS.
Mohammed zai maye gurbin Ahmed Rufa’i Abubakar wanda ya ajiye aikinsa a karshen makon da ya gabata.
Shi kuma Ajayi ya maye gurbin Yusuf Magaji Bichi wanda Buhari ya nada a shekarar 2018.
Wane ne Ambasada Mohammed Mohammed
Ambasada Mohammed ya kasance cikin ayyukan da suka shafi harkokin waje tun da ya fara aiki a hukumar ta NIA a shekarar 1995.
Ya rike mukamai da dama inda har ya kai mukamin Darekta, ya kuma zama shugaban ofishin jakadancin Najeriya a Libya.
Ya kammala karatunsa ne a Jami’ar Bayero da ke Kano a shekarar 1990, ya kuma yi aiki a Koriya ta Arewa, Pakistan, Sudan da kuma fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Wane Ne Mr. Adeola Ajayi
Mr. Adeola Ajayi ya rike mukamai da dama a hukumar ta DSS inda har ya kai mukamin Mataimakin Darekta-Janar a hukumar.
Ya rike mukamin Darekta a jihohin Bauchi, Enugu, Bayelsa, Rivers, da kuma Kogi
“Shugaba Tinubu na fatan sabbin shugabannin hukumomin za su yi aiki tukuru waje samar da sauyi a hukumomin biyu don a shawo kan matsalolin tsaro da ke addabar kasar ta hanyar hada kai da sauran takwarorin aikinsu na tsaro.” In ji Ngelale.