Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Da Ya Sa Kotun Faransa Ta Damka wa Kamfanin China Jiragen Shugaban Najeriya


Shugaba Macron, hagu, da Shugaba Tinubu, dama (Hoto: Dada Olusegun)
Shugaba Macron, hagu, da Shugaba Tinubu, dama (Hoto: Dada Olusegun)

“Babu shakka, kamfanin Zhongshan ya boye wasu bayanai ya kuma yaudari kotun Paris wajen ganin an ba shi wadannan jiragen shugaban kasa wadanda suka je kasar ta Faransa don a duba lafiyarsu.” In ji Onanuga.

Takaddama ta kaure bayan da wata kotu a birnin Paris na kasar Faransa ta yanke hukuncin mika wasu jiragen shugaban Najeriya uku ga wani kamfanin kasar China.

A ranar Alhamis rahotanni suka nuna cewa kotun ta ba kamfanin Zhongshan Fucheng Industrial Investment Co. Ltd jiragen bayan da ya shigar da karar neman karbe wasu kadarorin kasar a wasu sassan duniya a matsayin diyya ga wata kwangila da jihar Ogun ta soke ma kamfanin.

A shekarar 2015 jihar ta Ogun ta soke kwangilar gina wata kasuwa wacce a lokacin kamfanin na Zhongshan katanga kawai ya gina.

A shekarar 2007 aka ba kamfanin kwangilar.

Jiragen da kotun ta ba kamfanin na China sun hada da Dassault Falcon 7X, Boeing 737-7N6/BBJ da kuma A330-243 wadanda suke filin tashin jirage na Paris-Le Bourget da Basel-Mulhouse airports.

Gwamnatin Najeriya ta ce tana sane da kokarin da jihar ta Ogun ke yi wajen ganin an sasanta rikicin ta hanyar lumana a cewar wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Bayo Onanuga ya fitar a ranar Alhamis.

“Wannan mataki na tankwasa hannun gwamnatin Najeriya da kamfanin na China ya yi, shi ne mataki na baya-bayan daga cikin jerin matakan da ya dauka na karbe kadarorin Najeriya da ke kasashen waje.

“Babu shakka, kamfanin Zhongshan ya boye wasu bayanai ya kuma yaudari kotun Paris wajen ganin an ba shi wadannan jiragen shugaban kasa wadanda suka je kasar ta Faransa don a duba lafiyars.” In ji Onanuga.

A cewar Onanuga, kamfanin ya yi yunkurin daukan irin wannan mataki a kasar Birtaniya da Amurka, “amma abin ya ci tura.”

Gwamnatin jihar Ogun wacce ta nuna takaicinta kan wannan takaddama ta ce tana aiki tare da hadin kan gwamnatin tarayya wajen ganin an karbo wadannan jirage ba tare da bata lokaci ba a cewar wata sanarwar da kakakin gwamnatin jihar Kayode Akinmade ya fitar a ranar Alhamis.

“Muna takaicin wannan abin kunya da wannan al’amari ya janyo wa gwamnatin tarayya da Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma al’umar jihar Ogun.” In ji Kayode Akinmade.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG