Sanarwar da mashawarcin shugaban kasar na musamman akan harkokin yada labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga ya fitar a yau Litinin, ta bayyana hakan da samun gagarumar nasara a 2024 wacce ta sake karfafa fatan da ‘yan Najeriya ke da shi a kan gwamnatinsa.
“A yau, matatar mai ta Warri ta koma bakin aiki makonni bayan da kamfanin NNPCL ya farfado da matatar Fatakwal a watan Nuwamban da ya gabata daka iya tace ganga 60, 000 a kowace rana.
“Da sake farfado da matatar Warri bayan shafe dimbin shekaru bata aiki, Shugaba Tinubu ya sake bayyana aniyar gwamnatinsa ta bunkasa tace mai a cikin gida tare da mayar da Najeriya cibiyar hada-hadar albarkatun mai a nahiyar Afirka.
Cikin kwarin gwiwa Shugaba Tinubu ya kara da cewa kasancewar matatar Warri daka iya tace ganga 125, 000 ta danyen mai a kowace rana ta koma bakin aiki a kan kaso 60 cikin 100, shirin gwamnatinsa na tabbatar da samu da wadatuwar makamashi na tafiya yadda ya kamata.