Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matatar Man Fatakwal Ta Fara Tace Danyen Mai


Matakin na yau Talata ya kawo karshen gazawar wa’adin fara aikin matatar Najeriya dake jihar Ribas mai arzikin man fetur.

Matatar Fatakwal dake jihar Ribas a Najeriya ta fara tace danyen mai.

Babban jami’in yada labaran kamfanin man fetur na Najeriya (nnpcl), Femi Soneye, ne ya bayyana hakan.

A cewar Soneye a Talatar nan (yau) za a fara lodawa manyan motocin man, inda ya kara da cewa NNPCL na aiki tukuru wajen ganin matatar mai ta Warri “ta koma aiki nan bada jimawa ba”.

Matakin ya kawo karshen gazawar wa’adin fara aikin matatar Najeriya dake jihar Ribas mai arzikin man fetur.

Yayin hawansa kan mukamin a watan Agustan 2023, karamin ministan albarkatun man fetur (mai kula da bangaren mai) Heineken Lokpobiri yace matatar mai ta Fatakwal za ta fara aiki a watan Satumba kafin daga bisani aka mayar da lokacin zuwa watan Disamban shekarar da muke ciki.

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG