Shugaban kamfanin man fetur din Najeriya (NNPCL), Mele Kyari ne ya bayyana hakan yayin rangadin duba matatar daya gudanar a yau Litinin.
Matatar da aka kafa a 1978 karkashin kulawar NNPCL, an assasata ne da nufin samarda albarkatun man fetur ga kasuwannin yankunan kudanci da kudu maso yammancin Najeriya.
Matakin ya kawo karshen gazawar wa’adin fara aikin matatar Najeriya dake jihar Delta mai arzikin man fetur.
Hakan na zuwa ne biyo bayan fara tace danyen man fetur da matatar man Fatakwal a ranar 26 ga watan Nuwamban 2024.
Dandalin Mu Tattauna