Tinubu Ya Ce ‘Ilimantar’ Da Matasa Zai Kawo Karshen Matsalolin Tsaro

Shugaban Kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya fada ranar Talata cewa gwamnatinsa za ta fara "gagarumin shirin ilimantarwa" ga matasa a matsayin daya daga cikin hanyoyin magance karuwar satar mutane don neman kudin fansa da ke barazana ga babban birnin kasar tare da yankunan Arewacin kasar da ke fama da rikici.

WASHINGTON, D. C. - Shugaba Tinubu ya lashe zaben shekarar da ta gabata bayan ya yi alkawarin kawar da matsalar rashin tsaro a kasar da ke yammacin Afirka. Sai dai har yanzu ana ci gaba da kai munanan hare-hare musamman a arewacin kasar, inda babban birnin tarayya Abuja ke samun karuwar sace-sacen mutane a manyan tituna da kuma gidaje a 'yan makwannin nan.

Tinubu ya yi Allah-wadai da sace-sacen da aka yi a matsayin "mummunan al'amari mai tayar da hankali, da kuma mugunta" ya kuma bayyana samar da ilimi a matsayin "maganin matsalolin da ke ta da hankalin al'ummar kasar," a cewar wata sanarwa daga kakakin shugaban kasar, Ajuri Ngelale.

"Babu wani makami da zai yaki talauci da ya kai karfin karatu," in ji sanarwar. "Hukumomin tsaro suna aiki tare da tura dakaru don magance kalubalen da ake fuskanta nan da nan, yayin da kuma za'a samar da dukkan abubuwan da ake buƙata, da manufofi da tsare-tsare nan ba da jimawa ba don ilimantar da matasan Najeriya."

Tuni dai jami'an tsaron Najeriya ke fafatawa da 'yan tawayen jihadi a yankin arewa maso gabas baya ga kungiyoyin da ke dauke da makamai wadanda galibi ke aiwatar da kashe-kashe da sace-sace a wasu al'ummomin yankunan karkara a arewa maso yamma da tsakiyar kasar.

Yanzu haka mazauna wajen babban birnin kasar sun fara yin kaura a daidai lokacin da ake samun yawaitar sace-sacen mutane don neman kudin fansa da ake zargin 'yan bindiga ne daga jihohin da ke makwabtaka da birnin.

Manazarta sun ce Tinubu bai yi wani abin a zo a gani ba wajen magance matsalolin tsaro.

-AP