ABUJA, NIGERIA - Jawabin shugaba Bola Ahmed Tinubu na nuna zummar sa ta neman hadin kai da sashen majalisar dokoki wajen gudanar da lamurran mulki, don a ganinsa, zaman doya da manja tsakanin sassan biyu na gwamnati kan kawo cikas ga tsarin dimokradiyya.
In za'a iya tunawa an sami rashin fahimtar juna tsakanin gwamnatin Muhammadu Buhari a wa’adin mulkinta na farko da majalisar dokoki ta 8 a karkashin shugabancin Bukola Saraki ba.
To sai dai an sami sauyi a karshen wa’adin mulki na 2 da majalisa ta 9 wacce za ta gama aiki karkashin Ahmad Lawan, da ya sa aka dauke ta a matsayin ‘yar amshin shatar gwamnatin da ta shude.
Sabon dan majalisar dattawa, Sanata Ahmed Aliyu Wadada, wanda tsohon ‘dan majalisar wakilai ne, ya ce sam ba za su zama ‘yan amshin shata ba.
Wadada ya ce sun kuduri aniyar aiki tare da wannan sabuwar gwamnati akan abin da za ta yi na kyautata wa al'umma, kuma wannan abu ne mai kyau, amma kuma idan ta kauce hanya, shi da kansa zai jagoranci yi mata bore, domin ba abin da ya kawo su majalisa ba kenan.
Wadada ya ce idan sun hada kai wajen gudanar da mulki mai amfani, ba shi ne zama 'yan amshin shata ba.
Shi kuma ‘dan majalisar wakilai daga Jos/Bassa a jihar Filato Muhammad Adam Alkali ya nuna gamsuwa ne da salon mulkin Buhari da kuma shigowar Tinubu.
Adam ya ce ya yaba da irin mulkin Muhammadu Buhari amma yana da shawara ga sabon shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, inda ya yi kira ga sabon shugaban da ya fara kokarin hada kan ‘yan kasa, domin wanan zabe da aka gudanar ya raba kan kasar sosai.
Shugaban jam’iyyar SDP da ya halarci taron rantsarwar, Shehu Gabam ya shawarci ‘yan majalisar dokoki da su rika duba bukatun kasa fiye da na jam’iyya wajen gudanar da ayukan su na dokoki.
Gabam ya ce sun tattauna da ‘yan majalisun cewa su tabbatar an ba kananan hukumomi cin gashin kan su domin su ne kusa da al'umma. Gaban ya ce in an yi haka al'umma za su mori romon dimokradiyya.
A watan nan na Yuni mai shigowa ne za a rantsar da sabuwar majalisar, wacce itace ta 10 a tarihin dimokradiyyar Najeriya.
Saurari cikakken rahoto daga Medina Dauda:
Your browser doesn’t support HTML5