Shugaban Najeriya Bola Ahmad Tinubu ya bukaci dukkanin masu ruwa da tsaki a zaben gwamnan jihar Edo mai zuwa dasu gudanar da ayyukansu cikin lumana da mutunta juna.
An tsara gudanar da zaben ne a gobe Asabar, 21 ga watan Satumbar da muke ciki.
Sanarwar da mashawarcin shugaban kasa na musamman akan harkokin yada labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga, ya fitar a yau Juma’a, tace shugaban kasar ya roki ‘yan takarar gwamnan da jam’iyun siyasa da magoya bayansu dasu mutunta tsarin dimokiradiya da kuma zabin mutane.
Shugaba Tinubu ya jaddada cewa tsarin dimokiradiya na bunkasa ne a kan wayewa da juriya da hakuri da kuma mutunta ka’idojinsa.
Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar dasu kasance cikin lumana da mutunta juna a yayin zaben.
Haka kuma, Tinubu ya umarcesu dasu warware kowace irin takaddama ta hanyar lumana ta hannun hukumomin da doka ta amince dasu.